Home Labaru Juyin Zamani: Majalisar Wakilai Za Ta Yi Zaman Bankwana A Ranar Alhamis

Juyin Zamani: Majalisar Wakilai Za Ta Yi Zaman Bankwana A Ranar Alhamis

329
0
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19

Majalisar wakilai ta takwas a tarihin dimokradiyyar Nijeriya, za ta kawo karshen nauyin da ya rataya a wuyan ta, yayin zaman ban-kwana da za ta gudanar a Alhamis, 6 ga watan Yuni na shekara ta 2019.

Mukaddashin mai rikon sandar iko ta majalisar Patrick Giwa ya bada tabbacin hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja.

Patrick Giwa, ya ce majalisar wakilai za ta fara gudanar da zaman ta na ban-kwana da misalin karfe 11.00 na safiyar ranar Alhamis a zauren majalisar da ke Abuja.

An dai bukaci dukkan ‘yan majalisar da manyan baki su kasance sun sama wa kawunan su wurin zama gabanin fara gudanar da zaman kamar yadda rahotanni su ka bayyana.