Home Labaru Raha: Duk Da Kin Zabe Na Da ‘Yan Abuja Su Ka Yi...

Raha: Duk Da Kin Zabe Na Da ‘Yan Abuja Su Ka Yi Za Mu Tabbatar Mun Inganta Birnin – Buhari

333
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana wa tawagar da ta kai ma shi gaisuwar Sallah a fadar shi da ke Abuja cewa, duk da mutanen birnin tarayya ba su zabe shi a zaben shekara ta 2019 ba zai maida hankali wajen inganta rayuwar su.

Tawagar, wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, sun kai ziyarar ne domin taya shugaba Buhari murnar karamar sallah.

A jawabin sa, Buhari ya yaba wa Osinbajo bisa kwazo da maida hankali da ya yi wajen tallata manufofin gwamnati, ya na mai cewa idan ba haka ya yi ba to za a iya samun matsala, domin zai zamo kamar gwamnati ba ta aikin komai kenan.

A cikin barkwanci, shugaba Buhari ya ce wa sanata Philip Aduda da ke wakiltar Abuja a majalisar dattawa, cewa ya hango shi amma fa bai manta da yadda su ka tabbatar ya fadi zabe a Abuja ba.

Shugaba Buhari, ya ce duk da kin zaben sa da mutanen Abuja su ka yi, ba zai sa a ki maida hankali wajen tabbatar da ganin garin ya inganta ko ya shahara ba, domin mutanen da ke cikin birnin su wataya da kuma kasa baki daya.

Leave a Reply