Home Labaru Jin Kai: Za A Fara Jefa Kayan Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira...

Jin Kai: Za A Fara Jefa Kayan Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira Ta Jiragen- Minister Saadiya

458
0

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na fara bai wa kauyukan arewa maso gabas agaji ta hanyar cilla wa ‘yan gudun hijira abinci ta sama.

Ministan kula da walwala da jin kan ‘yan kasa, Sadiya Farouk, ta shaida wa ‘yan jarida a Maiduguri.

A ranar Lahadi ta sanar da cewa za a fara yin amfani da jiragen sojin saman Najeriya domin wurga kayayyakin tallafi kamar su bargo da abinci.

Ta sanar da cewa akwai manyan matsalolin da suke fuskanta na kai wa ga jama’ar da ke cikin kauyuka. Hakan yasa tace za su fara Villa kayan ta jiragen sama ga kauyukan da motoci basu iya zuwa.

Yankin arewa maso gabas na Najeriya na daga cikin yankunan da ta’addanci da rashin kwanciyar hankali ya addaba a Najeriya.

Mayakan ta’addancin na Boko Haram sun kasance suna cin karensu babu babbaka a yankin tun a 2009.

Hakan ya kawo mutuwar jama’a masu yawa tare da sanya wasu suka bar gidajensu domin neman mafaka a sassa daban-daban na kasar nan har da ketare.

A wani labari na daban, a kalla mutum hudu cikin ‘yan gudun hijira mayakan Boko haram suka yi awon gaba da su a yayin da

Leave a Reply