Home Labaru Zaben Fidda Gwani: Wata Farfesa Ta Lashe Zaben Sanata A Jos

Zaben Fidda Gwani: Wata Farfesa Ta Lashe Zaben Sanata A Jos

306
0

Farfesa Nora Daduut ta sashen koyar da harshen Faransanci na Jami’ar a Jos jihar  Filato ce, ta lashe zaben fid da takararar zaben cike gurbin kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Filato ta kudu,  a Jihar Filato karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne, bayan da ta kayar da wadanda suka fafata da ita a takarar.

A yanzun dai za a gudanar da zaben cike gurbi na Sanata a mazabar ne, sakamakon rasuwar tsohon Sanatan da ke wakiltar ta, Sanata Ignatius LongJan a wata Fabarairun da ya gabata.

Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin shirya Zaben, Habu Isa Ajiya, ya yi bayanin cewa Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne da kuri’u 1,936.

Damian Shekarau ya samu kuri’u 61, Farfesa Doknan Shenni ya sami kuri’u 60 sai kuma Farfesa Emmanuel Garba wanda ya sami kuru’u 16.