Home Labarai Hukuncin Babbar Kotu: Shugaban EFCC Ya Ce Zai Daukaka Kara

Hukuncin Babbar Kotu: Shugaban EFCC Ya Ce Zai Daukaka Kara

154
0

Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar sa zata daukaka kara bisa hukuncin wata babbar kotun tarayya dake zama a birnin Abuja, da ta ce ta tura shi gidan gyara hali na Kuje bisa laifin rashin biyayya ga hukuncin kotun da ta ce a mayar wa wani mutum wasu kudadde da motor sa.

Abdurrasheed Bawa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ta wayar tarho ga Muryar Amurka a game da labarin aika shi kurkukun Kuje da ya karade kafaffen yanar gizo, yana mai cewa ba shi ne shugaban hukumar EFCC ba a lokacin da lamarin ya faru a shekarar 2018.

A wani hukunci da ta yanke a ranar Talata ne, mai shari’a Chizoba Oji, ta bayyana cewa shugaban hukumar EFCC na lokacin, ya yi watsi da umarnin da kotun ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2018, inda ta umurci hukumar da ta mayar wa wani mai mota kirar Range Rover kayan shi ta kuma biya shi Naira miliyan 40.

Mai shari’a Oji ta kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya tabbatar da cewa an aiwatar da umurnin kotun nan take.

Leave a Reply