Home Labaru Kasuwanci Karancin Man Fetur:  IPMAN Ta Yi Kiran Kara Farashi

Karancin Man Fetur:  IPMAN Ta Yi Kiran Kara Farashi

38
0

Kungiyar dalilan man fetur ta Najeriya, IPMAN, ta bukaci a yi karin kudin man fetur a hukumance muddin ana so a saukaka wahalhalun samun mai da kuma kawo karshen karancin sa a faɗin Najeriya.

IPMAN ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ‘yan kasa ke cigaba da fuskantar karancin mai a galibin jihohin arewa da nanbabban birnin tarayya Abuja.

An kwashe ‘yan makonni dai ana fama da karancin man fetur, duk da irin matakan da gwamnati ke ɗauka domin saukaka matsalar.

Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin man fetur ba a Najeriya.

Wannan ne ya sa farashin ya sauya a cikin watanni baya, abin da ya kawo sauki a wancan lokaci, sai dai makonni bayan hakan sai wahalar ta sake kunno kai kuma har yanzu ana cikin ta.