Home Home Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Shirin Agajin Al’umma Na Tsawon Shekaru Biyar

Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Shirin Agajin Al’umma Na Tsawon Shekaru Biyar

165
0

Gwamnatin Tarayya, ta ƙaddamar da wani ingantaccen shiri na tsawon shekaru biyar da Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Inganta Rayuwa za ta yi aiki da shi tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2025.

Kundin shirin dai ya na ƙunshe da tsare-tsaren jin-ƙai da
hanyoyin samar da yadda za a yi aiki tare a ayyukan jin-ƙai na
cikin gida da na ƙasar waje.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osibajo ya ƙaddamar
da shirin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, wanda ya samu
wakilcin Mataimakin Shugaban Ma’aikata na fadar shugaban
ƙasa Adeola Rahman Ipaye.

Ya ce kundin da aka ƙaddamar wani babban ci-gaba ne ga
Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da ma ita kan ta gwamnatin
tarayya.

Tun da farko a wajen taron, Ministar Jin-Kai Sadiya Umar
Farouq, ta ce kirkiro da kundin ya zama wajibi, domin a samar
da alƙiblar da za a fuskanta wajen sauke nauyin da ya rataya a
wuyan ma’aikatar.

Leave a Reply