Home Home Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da 2 Daga Cikin Abokan Harkallar Abba...

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da 2 Daga Cikin Abokan Harkallar Abba Kyari

63
0

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, ta dakatar da ACP
Sunday Ubua da ASP James Bawa daga aiki da kuma mukaman su da ayyukan ofisoshin su daga ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu na shekara ta 2022.

Jami’an ‘yan sandan biyu dais u na aiki ne a karkashin DCP
Abba Kyari da aka dakatar a cikin tawagar leken asiri ta IRT.

Lamarin dai ya na faruwa ne, yayin da ake ci-gaba da binciken
Abba Kyari da tawagar sa bisa zargin kulla harkallar miyagun
kwayoyi ta kasa da kasa.

Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani, ya an kuma yi
zargin cewa ma’aikatan su na da hannu wajen kama hodar ibilis,
tare da mika su ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi
ta kasa NDLEA.

Hukuncin hukumar ya na kunshe ne a cikin wata wasika da ta
aike wa shugaban ‘yan sandan Nijeriya, wadda ke dauke da sa
hannun mai shari’a Clara B. Ogunbiyi mai ritaya na kotun koli,
da tsohon shugaban ‘yan sandan Nijeriya Musiliu Smith.