Home Labaru Gwamnatin Jihar Bauchi Za Ta Ƙirƙiro Rundunar Tsaro Ta Musamman

Gwamnatin Jihar Bauchi Za Ta Ƙirƙiro Rundunar Tsaro Ta Musamman

78
0

Gwamnatin jihar Bauchi, ta ce za ta dauki akalla matasa dubu
20 aiki, domin a yaki matsalar tsaro tare da tabbatar da zaman
lafiya da kwanciyar hankali, a karkashin wata rundunar tsaro
da za ta kirkiro ta musamman a jihar.

Wata majiya ta ce, rundunar tsaron za ta kasance kamar wadda jihohin kudu maso yammacin Nijeriya su ka kirkiro wato Amotekum.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya bayyana matakin, jim bayan an sake rantsar da shi a wa’adi na biyu.

Sanata Bala Mohammed, ya ce rundunar za ta taimaka wa tsarin tsaron da tuni ake da shi a kananan hukumomin jihar, kuma za ta kunshi matasa dubu 20 da za a fara dauka a karon farko.

Leave a Reply