Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Rabon Kayan Tallafi – Buhari

Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Rabon Kayan Tallafi – Buhari

295
0
Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Rabon Kayan Tallafi - Buhari
Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Rabon Kayan Tallafi - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta ci gaba da rabon kudi da kayan abinci ga talakawa a daidai lokacin da aka kara wa’adin dokar hana shiga da fita a jihohi Legas da Ogun da kuma Abuja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Buhari ya sanar da tsawaita dokar da karin makonni 2 a jawabinsa ga ‘yan Nijeriya a daren Litinin din da ta gabata.

Shugaban ya ce gwmantinsa ta kara wa’adin dokar ne sakamakon shawarwarin da ya samu daga kwararru, domin dakile yaduwar cotar COVID-19.

Ya kara da cewa, tsawaita dokar ya zama tilas domin kare yaduwar cutar Coronavirus a Nijeriya, musamman duba da yadda aka fi samun masu cutar jihar Legas da kuma Abuja.

Cibiyar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC ta ce mafi yawanci daga cikin mutum fiye da 300 da ke dauke da cutar a Nijeriya, sun fito ne daga Legas da Abuja. 

Buhari ya ce sakamakon tsawaita dokar hana fitar, Gwamnatin Tarayya za ci gaba rabon tallafin kudi d kayan abincin ga talakawa, domin rage musu radadin halin da ake ciki.