Home Labarai Gazawa:Kungiyar  NANS Ta Bukaci A Sallamin Shugaban NNPC Da Minstan Lantarki

Gazawa:Kungiyar  NANS Ta Bukaci A Sallamin Shugaban NNPC Da Minstan Lantarki

110
0
NANS 2
NANS 2

Kungiyar Dalibai ta kasa wato NANS ta yi kira gaShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
da a kori Shugaban NNPC Mele Kyari da Ministan Wutar Lantarki Adelabu, ko su shirya
zanga-zanga a fadin ƙasar nan


Dangane da kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta na rashin samun daidaiton wutar lantarki, tsadar farashin kaya, da matsalar man fetur da ake fama da shi, 

NANS ta yanke shawarar shirya zanga-zanga a fadin kasar a Ranar Talata, 7 ga Mayu, 2024, kuma ta nemi goyon bayan ‘yan Najeriya dasu Basu Goyan Baya. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Sanata Akinteye Babatunde Afeez, ya fitar Shugaban majalisar dattawar NANS, da shugabannin yankunanta guda biyar suka amince da su, sun nuna matukar damuwa cewa dukkan ayyukan shugabancin Kyari da Adelabu sun taimaka wajen karkatar da albarkatun makamashi.

Wannan lamari dai ya kara ta’azzara halin da al’ummar kasa ke ciki a halin yanzu, kamar yadda ‘yan Najeriya da dama suka bayyana.

Leave a Reply