Kamfanin man fetur na kasa (Nigerian National Petroleum Company Ltd) ya bayar da
tabbaci ga ‘yan Najeriya cewa za a shawo kan matsalar karancin man fetur da layukan
da ake fama da su A gobe Laraba.
Babban jami’in sadarwa na NNPC Olufemi Soneye, shine ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya. Mista Soneye ya ruwaito cewa kamfanin a halin yanzu ya mallaki rarar kayayyaki sama da lita biliyan 1.5, wanda ya isa ya ci gaba da gudanar da ayyuka na tsawon kwanaki 30.
Ya kara da cewar sun kamfanin ya samu cikas na tsawon kwanaki uku a wajen rabon kayayyakin, sakamakon matsalolin kayan aiki, Wanda tun daga lokacin aka shawo kan matsalar.