Home Labaru Kuskure: Jirgin Yakin Nijeriya Ya Yi Wa Kananan Yara Aman Wuta A...

Kuskure: Jirgin Yakin Nijeriya Ya Yi Wa Kananan Yara Aman Wuta A Jihar Borno

1710
0

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukan su dai-dai lokacin da  jirgin yakin Nijeriya ya yi masu jefa wuta bisa kuskure a yakin Sakotoku da ke karamar hukumar Dambo da ke jihar Borno.

Wata majiya ta ce, wadanda suka mutu a harin sun hada da mata da kuma kananan yara da ke wasa a karkashin bishiyar mangwaro.

Majiyar ta kara da cewa, an jefa bamabaman ne bayan rundunar sojin sama ta Nijeriya nta samu labarin taruwar ‘yan Boko Haram a kauyen, lamarin da ya sa aka shirya musu luguden wuta, sai dai inda ya kamata a kai harin shine wani yanki a Korongilum da ke makwabtaka da yankin Sakotoku da kusan nisan kilomita 12.

Haka kuma, majiyar ta ce, a kwai yuwuwar an samu gibi a musayar bayani tsakanin sojin sama da na kasa, a lokacin da jiragen rundunar sojin sama suka jefa bamabamai a kauyen, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 17 da raunata wasu da dama.

Kawo yanzu dai, an garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin runduna ta 25 da ke Damboa, sannan wadanda ke cikin mawuyacin hali an mika su zuwa Maiduguri.