Home Labaru ‘Yan Daba Sun Tayar Da Rikici Saboda Dokar Hana Fita

‘Yan Daba Sun Tayar Da Rikici Saboda Dokar Hana Fita

312
0
‘Yan Daba Sun Tayar Da Rikici Saboda Dokar Hana Fita
‘Yan Daba Sun Tayar Da Rikici Saboda Dokar Hana Fita

Hatsaniya ta barke a wasu sassam Jihar Legas biyo bayan tsaiwaita dokar zaman gida da Gwamantin Tarayya ta yi a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da tsawaita dokar ne  domin hana yaduwar cutar COVID-19 a jihohin, matakin da bai yi wa wasu mazuna yakin Legas dadi ba.

Wasu fustattun matasa fiye da 100, dauke da makamai sun yi ta shiga unguwanni a jihar Legas inda suka rika huce fushinsu a kan mutanan da ba su ji ba su gani ba.

Ta’adin na daren Litinin ya yi kama da abin da ya auku a ranar Lahadi, inda da tsakar rana ‘yan daba suka rika yi wa jama’a kwace, tare fasa shaguna da gidajen suna kwasan kaya a jihohin Legas da Ogun.

Ta’addancin ‘yan daban dauke da makamai ya tayar da hankulan mazauna yankunan Mangoro da Ogba da Agege da Iyana Ipaja da kuma Dopemu.