Home Labarai Musayar ‘Yan Wasa: Man City Na Neman Ait-Nouri, Man Utd Na Son...

Musayar ‘Yan Wasa: Man City Na Neman Ait-Nouri, Man Utd Na Son Gyokeres

29
0
skysports wolves rayan ait nouri 5694288
skysports wolves rayan ait nouri 5694288

Manchester City ta fara tattaunawa da Wolves a kan yuwuwar sayen dan bayan Algeria Rayan Ait-Nouri, mai shekara 22.

Tottenham ta taya dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo a kokarin da take yi na riga Manchester United saye dan wasan dan Ingila mai shekara.

Newcastle na duba yuwuwar daukan Adarabioyo tare da Lloyd Kelly dan bayan Bournemouth kasancewar kwantiragin ‘yan wasan biyu ‘yan Ingila zai kare a bazara.

Manchester United na nuna sha’awarta a kan sayen mai kai hari na Sporting Lisbon Viktor Gyokeres amma kuma tana fargabar Liverpool ka iya yi mata nakasu wajen sayen dan Sweden din mai shekara 25.

Liverpool za ta iya sayen dan bayan Sporting Lisbon Goncalo Inacio, dan Portugal mai shekara 22, a kan fam miliyan 40.

Leave a Reply