Home Labaru Kiwon Lafiya Zazzabin Cizon Sauro: Mutum 7 Sun Rasu A Kano

Zazzabin Cizon Sauro: Mutum 7 Sun Rasu A Kano

34
0
ways to prevent malaria 0
ways to prevent malaria 0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta karyata rahotannin barkewar wata sabuwar cuta a kauyen Gundutse da ke karamar hukumar Kura.

Jami’in yada labarai na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, a wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya, ya ce mutane bakwai ne suka mutu a cikin al’ummar sakamakon tsananin zazzabin cizon sauro da taifod, ba wata sabuwar cuta ba.

Ya bayyana cewa, bayanan da aka samu daga bincike da sa ido na masana DSNR a karamar hukumar sun nuna cewa, sananniyar cuta ce wato zazzabin cizon sauro da taifod ce da ta bulla a cikin al’ummar a cikin watan Ramadan.

A halin da ake ciki, Abdullahi ya kara da cewa, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki sun dauki matakan shawo kan lamarin yayin da ake ci gaba da sa ido.

Leave a Reply