Home Labarai Ta’Addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Hakimi A Fadar Sa A Jihar Taraba

Ta’Addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Hakimi A Fadar Sa A Jihar Taraba

32
0

’Yan bindiga sun kashe Sarkin Sansani da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Abdulmudallib Kankada.

Maharan sun shiga fadar hakimin ne da misalin karfe 9 na daren Alhamis, inda suka yi masa ruwan harsashi, suka kashe shi nan take.

Wani mazaunin garin na Sansani, ya shaida cewa a cikin dakin hakimin ’yan bindigan suka kashe shi.

A cewar sa, a  kan babura suka shiga garin, amma suka boye buburan ne sa da fadar sarkin suka shiga ba tare da kowa ya sani ba.

Ya ce daya daga cikin matan sarkin ce ta shiga dakin ta tarar da an kashe mijin nata yana kwance cikin jini, shi ne ta sanar wa sauran matan daga nan kuma labarin ya bazu cikin gari.

Tuni dai aka yi jana’izar sa bayan sallar Juma’a a fadar sa.

An taba sace sarkin shekarun biyu da suka wuce kuma sai da aka biya kudin fansa aka sako shi.

Sarkin Sansanin shine na bakwai a jerin sarakunan gargajiya da ’yan bindiga suka kashe a ’yan shekarun nan a Jihar Taraba.

Leave a Reply