Home Labaru Kimiyya Jihohi 14 Da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa – NEMA

Jihohi 14 Da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa – NEMA

65
0

Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Kasa NEMA, ta zayyana
jihohi 14 da yankuna 31 da ka iya fuskantar ruwan sama mai
karfi da zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga
watan Yuli na shekara ta 2023.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hukumar na jihar Ibrahim Farinloye.

Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.

Jihohin da lamarin zai shafa kuwa sun hada da Filato da Kano Sokoto da Delta da Kaduna da Akwa Ibom da Adamawa da Katsina.

Sauran sun hada da Kebbi da Zamfara da Borno da Jigawa da Kwara da kuma Neja.

Farinloye ya gode wa Hukumar Hasashen Ruwan Sama da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya da ke Abuja bisa bayyana bayanan daminar bana a kan lokaci.

Leave a Reply