Home Labarai Shari’ar Zargin Ta’Addanci: Kotu Ta Hana Bada Belin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah

Shari’ar Zargin Ta’Addanci: Kotu Ta Hana Bada Belin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah

22
0
Bodejo Miyetti Allah
Bodejo Miyetti Allah

Kotu ta hana belin Shugaban Shugaban Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore,
Bello Boɗejo, bayan da ya nemi a bada belin sa a Babbar Kotun da ke Abuja.


Boɗejo dai ya na tsare ne a magarƙamar Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji (DIA), a Abuja, kuma ana tuhumar sa da laifin ta’addanci. Gwamnatin Najeriya na zargin sa da kafa ƙungiya ta zaratan Fulani tsantsa, ba bisa ƙa’ida ba da Sunan ta Ƙungiyar Zaman Lafiya.

Bello Boɗejo ya kafa Ƙungiyar Zaman Lafiya a garin Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa. 


An gurfanar da Boɗejo a kotu tare da zargin sa da laifuka uku, waɗanda Antoni Janar na Tarayya ya gurfanar da shi kan zargin Karya Dokar Ta’addanci ta 2022. Sai dai kuma Boɗejo ya ƙaryata dukkan zarge-zargen da ake yi masa.

Leave a Reply