Home Labaru Ilimi Limanci: Sheikh Yasser Dossary Ya Dawo Masallacin Harami

Limanci: Sheikh Yasser Dossary Ya Dawo Masallacin Harami

154
0

Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdul Rahman al-Sudais, ya sanar da dawowar Sheikh Yasser Dossary da wasu limamai biyu.

Sheikh Sudai ya sanar cewa Sheikh Yasir zai ci gaba da limanci a Masallacin Harami da ke Makkah.

Ya ce sauran limamn biyu, su ne Sheikh Khalid Muhanna da kuma Sheikh Ahmad Hudhaify, kuma za su ci gaba da limanci ne a Masallacin Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi Wa Sallama da ke Madina.

Wannan albishir daga Sheikh Sudais ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin fara azumin watan Ramadan na bana.

A yanzu dai adadin limaman masallacin Harami zai sake komawa 8 da suka kunshi Sheikh Abdur Rahman As Sudais, da  Sheikh Abdullah Awad Al Juhany, da Sheikh Maher Al Muaiqly, da Sheikh Bandar Baleelah, da Sheikh Faisal Ghazzawi, da Sheikh Saleh Al Humaid, da Sheikh Usaamah Khayyat da kuma Sheikh Yasser Dossary.

A Shekarar 2015 Sheikh Dawsary ya fara limancin sallar Taraweeh a Masallacin Harami a matsayin bakon liman, kafin shekarar 2019 Masarautar Saudiyya ta nada shi a matsayin cikakken limami, wanda za a rika sabunta kwangilar sa bayan shekara hudu.

A baya dai ana fargabar malaman ba za su yi limanci ba a watan Ramadan, saboda karewar wa’adin kwantiragin su na shekara huɗu a masallacin.

Leave a Reply