Home Labaru Olympics: Bikin Kunna Wutar Gasar Ya Gudana A Birnin Olympia

Olympics: Bikin Kunna Wutar Gasar Ya Gudana A Birnin Olympia

29
0
260314 thomasbachiocpres
260314 thomasbachiocpres

A Yau Talata aka kunna wutar gasar Olympics da birnin Paris ke shirin karɓa nan da ‘yan watanni.

Bikin na gargajiya ya gudana ne a garin Olympia mai tsohon tarihi da ke Girka, matakin da ke nuna kai wa gaɓar ƙarshe na shirye-shiryen da aka shafe shekaru bakwai ana yi kan gasar da za a fara a ranar 26 ga watan Yuli.

Jarumar fina-finan kasar Girka Mary Mina, da aka zaɓa a matsayin jagorar bikin gargajiyar ce ta kunna wutar Olympics ɗin, gasar da karo na uku kenan da Faransa za ta karɓi baƙuncinta a birnin Paris bayan hakan da ta yi a shekarun 1900, da kuma 1924.

Yayin jawabin da ya gabatar shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na duniya Thomas Bach, ya ce ko shakkah babu mutane sun kosa a fara wasannin motsa jikin domin ɗebe musu kewa daga tashe-tashen hankulan da suke ƙaruwa da suka kunshi, ta’addanci da kuma munanan labarai.

A makon da ya gabata shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a buƙaci Rasha ta tsagaita buɗe wuta a Ukraine yayin gudanar gasar ta Olympics, kamar yadda aka saba mutunta wasannin a lokutan baya, sai dai Rasha ta ki amincewa da tsarin bisa zargin cewa Ukraine za ta iya amfani da damar wajen sake kintsawa yakin da suke gwabzawa.

Leave a Reply