Home Labaru Harin Isra’Ila: EU Ta Lafta Sabbin Takunkumai Kan Iran

Harin Isra’Ila: EU Ta Lafta Sabbin Takunkumai Kan Iran

140
0
Mr Charles MICHEL President of the European Council
Mr Charles MICHEL President of the European Council

Shugabannin kasashen EU sun cimma jituwar amincewa da lafta sabbin takunkumai kan Iran game da harin da ta kai Isra’ila a karshen mako.

A daren jiya Laraba ne shugaban hukumar gudanarwar Turai Charles Michel ya sanar da matakin sabbin takunkuman na Tehran wadanda za su shafi kamfanoni da daidaikun mutane.

Matakin na EU na zuwa a dai dai lokacin da ministocin wajen kasashen G7 ke wani taro a tsibirin Capri na Italiya taron da shi ma ya mayar da hankali kacokan ga rikicin yankin gabas ta tsakiya musamman hare-haren na Iran kan Isra’ila a makon jiya.

Taron wanda aka faro jiya Laraba za kuma a kwashe kwanaki 2 ana yi gabanin karkarewa a ranar juma’ar makon nan, akwai yiwuwar ya kai ga matsayar lafta sabbin takunkumai kan Iran dai dai lokacin da ake fargabar yiwuwar Isra’ila ta mayar da martani kan Tehran.

Gamayyar kasashen na EU da na G7 sun ce sam hare-haren na Iran ba abin lamunta ba ne, wanda ke nuna dole a dakatar da kasar wadda tun tuni ke fuskantar tarin takunkuman karya tattalin arziki daga kasashe saboda shirinta na mallakar nukiliya.

Sai dai masana na ci gaba da gargadi kan abin da ka je ya zo, matukar Isra’ilan ta yi yunkuri mayar da martani kan Iran, wanda ka iya zama rincabewar rikicin gabas ta tsakiya.

Tun farko Isra’ila ta fara kai farmaki kan ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus a Syria tare da kisan tarin dakarun juyin-juya halin Tehran da ke ofishin lamarin da Iran ta sha alwashin daukar fansa.

Leave a Reply