Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Wata Cuta Da Ba A Gane Kanta Ba Ta Bullo A...

Annoba: Wata Cuta Da Ba A Gane Kanta Ba Ta Bullo A Sokoto

34
0
Asabe Balarabe Sokoto State Commissioner of Health
Asabe Balarabe Sokoto State Commissioner of Health

Yayin da cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya ke gudanar da bincike a kan wata cuta da ta bulla a Sakkwato, wadda ba a gane kanta ba, yanzu haka cutar na ci gaba da yaduwa .

A wannan ranar ta Alhamis ce dai ake sa ran babban daraktan cibiyar ya ziyarci Sakkwato don kara matsa kaimi ga binciken gano cutar da abinda ke kawo kamuwa da ita.

Tun a watan Maris da ya gabata ne aka samu bullar cutar, wadda ke kawo kumburin ciki da ciwon zuciya, a wasu yankuna na karamar hukumar mulkin Isa da ke gabashin Sakkwato, sai dai jami’an lafiya na yankin ba su kai rahoton bullar cutar ba, sai da aka kawo wasu da suka kamu da cutar a asibitin koyarwa ta jami’ar Usmanu Danfodiyo dake cikin birnin Sakkwato.

Kwamishinan lafiya ta jihar Sakkwato Asabe Balarabe ta nuna bacin rai a kan rashin sanar da bullar cutar da har ta kama mutane talatin da biyu, inda daga baya gwamnati ta sanar da hedikwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya don daukar matakin da ya kamata.

Cibiyar dai nan take ta aika da jami’anta domin gudanar da bincike, inda suka dauki samfurin abubuwa a yankunan da cutar ta bulla don bincike, sai dai kawo yanzu ba a kai ga gano abin da kawo cutar ba, acewar Dokta Nuhu Aliyu Dogon Daji, jami’i mai kula da yaduwar cututuka da annoba a jihar Sakkwato.

To sai dai duk da haka, jagoran ayarin kwararri masu kawo dauki na cibiyar hana yaduwar cututuka ta Najeriya Mr. Tajudeen Orowola, lokacin da yake yi wa mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Muhammad Idris bayani a kan cutar yace tuni sun tura dukan sanfurin da suka dauka a cibiyoyin gudanar da bincike a sassa daban daban kuma suna kan aikin binciken cutar.

Leave a Reply