Home Labaru Ilimi Gwamnatin Adamawa Ta Fitar Da Naira Biliyan 2.4 Domin Biyan Jarrabawar WAEC Da...

Gwamnatin Adamawa Ta Fitar Da Naira Biliyan 2.4 Domin Biyan Jarrabawar WAEC Da NECO

44
0

Gwamnatin jihar Adamawa ta ware Naira biliyan 2 da dubu
dari 4 domin biyan kudaden rajistar jarrabawar WAEC da
NECO ga wadanda su ka cancanta a fadin jihar.

Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonisikou ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Yola.

Ya ce, kudaden za a biya ne don yin jarrabawar kammala sakandare ta wannan shekara, inda ya ba da tabbacin cewa, shirin zai dore.

Ya kara da cewa, Gwamnatin jihar ta himmatu kwarai dagske kuma ta kuduri aniyar sauke nauyin biyan kudaden jarrabawar a kan iyaye.

A karshe Wonisikou ya ce, gwamnatin Fintiri ta fitar da Naira miliyan 500 domin biyan alawus-alawus na ‘yan asalin jihar da ke karatu a manyan makarantu a fadin Nijeriya.

Leave a Reply