Home Labaru Ayyukan jinkai: gwamnatin tarayya za ta mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 daga...

Ayyukan jinkai: gwamnatin tarayya za ta mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 daga nijar da kamaru

267
0
Refugees seeking for refuge
Refugees seeking for refuge

Kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira (NCFRMI), Tijjani Ahmed ne ya
bayyana haka ranar Talata a Abuja a karshen wani da aka shirya don mayar da ‘yan
gudun hijirar Najeriya gida.


Ya ce kimanin ‘yan gudun hijira 21,000 ne ke a ƙasar Chadi yayin da Kamaru ke da wasu 14,000. Ahmed ya ƙara da cewa za a mayar da mutane 6,000 daga Chadi zuwa gida yayin da za a tantance adadin waɗanda za a mayar da su daga Kamaru kafin a fara shirin wanda
ake sa ran kammalawa nan da watanni biyu masu zuwa.


“Muna shirin mayar da waɗanda suke da sha’awar komawa gida, an kuma ƙulla yarjejeniya tsakanin hukumar UNHCR da gwamnatin Kamaru da kuma gwamnatin tarayya kan batun mayar da mutanenmu gida daga Kamaru,” in ji shi. Ya ce ana tattaunawa da gwamnatin jihar Borno kan wajen da za a ajiye ‘yan Najeriya da za a mayar da su gida, inda ya ce a yanzu haka ana gina gidaje a Banki da Baga domin ajiye su

Leave a Reply