Femi Falana Ya bayyana cewa ministan wutar lantarki Yana bin tsarin asusun bada
lamuni na duniya IMF da bankin duniya ta hanyar kara kudin wutar lantarki Ga al’ummar
ƙasar.
Ya ƙara da cewa Ministan wutar lantarki yana aiwatar da ajandar IMF da Bankin Duniya, wadannan cibiyoyi sun dage cewa Gwamnatin tarayya ta kawar da duk wani tallafin da take bayarwa, wanda ya hada da na man fetur da wutar lantarki, tare da inganta dukkan ayyukan jin daɗin jama’a,
Gwamnati ba za ta iya ba da fifiko ga muradun ‘yan Najeriya ba tare da bin manufofin neman sassaucin ra’ayi da cibiyoyin Bretton Woods suka tsara.” Babban Lauyan na Najeriya ya kuma soki kasashen Yamma, musamman Amurka, da yin amfani da ka’idoji biyu. Ya kuma bayyana yadda suke bada Tallafin noma, makamashi, da man fetur, da kuma bayar da tallafi da lamuni ga dalibai mabukata, a lokaci guda kuma ya ba da shawarar a guji irin wannan matakin ga al’ummar Najeriya
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, yayi Gargadi ne A Jiya Litinin, inda ya bayyana cewa matukar ba a aiwatar da karin kudin wutar da aka shirya yi ba, kasar za ta fuskanci katsewar wutar lantarki cikin watanni uku masu zuwa.














































