Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba ya ƙaru zuwa dubu 33 da 37.
Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutuwar mutane 62 a cikin awanni 24 da suka gabata.
Sanarwar ma’aikatar ta ƙara da cewa adadin mutanen da suka jikkata tun ranar 7 ga Oktoba ya kai dubu 75 da 668.
Sojojin Isra’ila sun fara kai farmakin ne bayan harin na ranar 7 ga watan Oktoba da mayaƙan Hamas suka kai inda suka kashe kimanin mutanen Isra’ila 1,200.