Home Labaru Godswill Akpabio Da Tajudeen Abbas Sun Zama Shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya

Godswill Akpabio Da Tajudeen Abbas Sun Zama Shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya

100
0

‘Yan Majalisar Dattawa sun zabi tsohon gwamnan jihar Akwa
Ibom Sanata Godswill Akpabio a matsayin sabon shugaban
majalisar, yayin da ‘yan majalisar wakilai su ka Tajudeen
Abbas a matsayin shugaban su.

An dai yi zaben ne yayin kaddamar da majalisun dokokin biyu, inda Akpabio ya samu kuri’u 63 a fafatawar da ya doke tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari da ya samu kuri’a 46.

A majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya samu kuri’u 353, inda ya kada tsohon mataimakin shugaban majalisar Ahmed Idris Wase da dan majalisa Sani Jaji, wadanda su ka samu kuri’u uku kowannen su.

Haka kuma, an zabi Benjamin Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai, yayin da Sanatoci su ka zabi Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Leave a Reply