Home Home Fintiri Ya Rantsar Da Bamanga Tukur Sabon SSG A Adamawa

Fintiri Ya Rantsar Da Bamanga Tukur Sabon SSG A Adamawa

306
0

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya rantsar da Sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Dakta Amos Edgar.

Haka kuma, gwamnan ya shaida rantsar da kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati Barista Afraimu Jingi, da babban jami’i mai binciken kudi Usman Ahmad, da shugaban ma’aikata Shehu Isah Ardo, wanda shugabar alkalan jihar Hafsat Abdul-Rahman ta jagoran ta.

Da ya ke jawabi yayin karbar rantsuwar, gwamna Fintiri ya bayyana kwarin gwiwa akan mutanen da ya ba mukaman, ya na mai fatan za su yi aiki da fahimta da yarda da juna da daukar matakan da za su kawo ci-gaba domin jama’ar Adamawa.

Da ya ke jawabi a madadin wadanda su ka karbi rantsuwar, Sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, ya gode wa gwamnan da ya ba su damar su yi wa al’ummar jihar aiki, sannan ya yi alkawarin gudanar da aiki bisa gaskiya da adalci, ta yadda jama’a za su amfana da mukaman da aka ba su.

Leave a Reply