Home Labaru Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Hukumar Kashe Gobara A...

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Hukumar Kashe Gobara A Legas

387
0
DSP Bala Elkana,Kakakin Rundunar 'Yan Sanda Na Jihar Legas
DSP Bala Elkana,Kakakin Rundunar 'Yan Sanda Na Jihar Legas

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da darektan hukumar kashe gobara a jihar Legas, Rasaki Musibau, tare da wasu mutane 9.

Rahotanni sun bayyana cewar lamarin ya faru ne a yayin da shugaban da mutanen ke kan hanyar su ta dawowa cikin garin Legas daga Epe, inda masu garkuwan suka tare kan gadar Itokin, tare da kaddamar da harin kwanton bauna akan mutanen da ke cikin motoci guda uku.

Mazauna yankin sun yi zargin cewar an sace wasu mutanen a cikin wata babbar mota, bayan motar ta tsaya domin sauke wasu fasinjoji akan hanyar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da sace Musibau da mutanen dake cikin tawagar sa, ya ce an sace mutanen bayan an yi wa motoci uku da suke ciki kwanton bauna.Sannan ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan da aka tura wurin sun yi nasarar samun wasu kayayyaki na mutanen da aka sace.

Leave a Reply