Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Ya Kamata Ayi Amfani Da Mafarauta – Sarki Sanusi

Yaki Da Ta’addanci: Ya Kamata Ayi Amfani Da Mafarauta – Sarki Sanusi

894
0
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Mai martana sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya ta yi amfani da mafarauta domin magance matsalar garkuwa da mutane a Arewacin Nijeriya.

Sanusi,  ya ce jihar Kano ta fuskanci irin wannan matsalar shekaru hudu da suka gabata, amma da suka yi amfani da mafarauta an samu nasara.

Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da tawagar mafarauta, sojoji, ‘yan sanda, da jami’an tsaro na Civil Defence domin kawo karshen garkuwa da mutane a jahohin Zamfara da Kaduna.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wani taro na shugabannin mafarauta a jihar Kano karkashin kungiyar masu kishin ci gaban jihar Kano, ya ce jihar Kano ta gwada irin hakan, kuma an sami nasara. Sanusi,  ya ce a cikin shekaru hudun da suka gabata, Kano ta Kudu ta kasance cikin fargaba saboda yawaitar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, amma cikin hikimar Allah mafarauta sun kawo kashen lamarin.