Home Labaru Fyade: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Mai Shekaru 26 Hukuncin Daurin Rai...

Fyade: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Mai Shekaru 26 Hukuncin Daurin Rai Da Rai

98
0

Kotun sauraren kararrakin cin zarafin mata da kananan yara
da ke Ikeja a jihar Legas, ta yanke ma wani Sunday George
hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin yi wa
‘yar makwafcin sa mai shekaru 12 fyade.

Alkalin kotun Abiola Soladoye, ya ce ya yanke hukuncin ne bayan fannin da ya shigar da kara ya tabbatar wa kotun cewa George ya aikata laifin da ake zargin sa akai.

Ya ce Yarinyar ta ce George makwafcin su ne, kuma ya fara yin fasikanci da ita ne a dakin sa idan ta shiga kallon talabijin, tare da ja mata kunnen kada ta gaya wa kowa.

Alkalin ya cigaba da cewa, mahaifin yarinyar da yarinyar ne su ka kai kara ofishin ‘yan sanda, sannan kotun ta samu tabbacin abin da George ya aikata daga hujjojin da rundunar ‘yan sandan ta gabatar.

Mai shari’a Soladoye, ya yi kira ga gwamnati ta cigaba da yin kira ga iyaye a kan sanin mahimmancin maida hankali da kula da ‘ya’yan su domin guje wa afka wa matsaloli irin haka.

Leave a Reply