Home Labaru Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Sha’Anin Tsaro

Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Sha’Anin Tsaro

266
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince ya ciyo bashin Dala miliyan 800.

Domin tabbatar da Nijeriya ta cigaba da rike muhimman
matakai da kuma ba shi damar karasa wa’adin sa a matsayin
babban jami’i a sashen ‘yan sandan kasa da kasa INTERPOL,
shugaba Buhari ya nada AIG Garba Baba Umar a matsayin
babban mai bada shawara a kan harkokin tsaro da ya shafi
hadin gwiwa da ‘yan sandan kasa da kasa da kuma yaki da
ta’addanci a ofishin ministan kula da harkokin ‘yan sanda.

Shugaba Buhari, ya ce AIG Garba Baba Umar ya taimaka wa Nijeriya sosai ta hanyoyi daban-daban. Buhari ya yi fatan cewa, a cikin shekara daya da ya rage ma shi zai kara azama da himma, zai kuma kara kwazo wajensamo wa Nijeriya kayan yaki da ‘yan ta’adda da kula da iyakoki da dakile ta’addanci a Nijriya.

Ya ce zai kuma taimaka wajen ganin Nijeriya ta kara samun muhimman mukamai a sashen ‘yan sandan kasa da da ma shigar da ‘yan Nijeriya ciki.

Wa’adin aikin AIG Garba Baba Umar dai zai kare ne a watan Nuwamba na shekara ta 2024, yanzu kuma ya zama babban mashawarci a kan lamarin tsaro da zai fara aiki daga ranar 16 ga watan Mayu na shekara ta 2023.

Leave a Reply