Home Labaru Diflomasiyya: Buhari Ya Ce Nijeriya Za Ta Ci Gaba Da Tallafa Wa...

Diflomasiyya: Buhari Ya Ce Nijeriya Za Ta Ci Gaba Da Tallafa Wa Makwabtan Ta

365
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Nijeriya za cigaba da taimakawa makwabtan ta inda bukatar hakan ya taso.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Guinea Job Obiang Esono Mbengono a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya ce Nijeriya da Guinea na da alaka mai karfi a tsakanin su, kuma za su ci gaba da makwabtaka mai nagarta har abada.

Shugaba Buhari ya kuma nuna farin cikin sa ga jakadan mai barin gado da ya kwashe shekaru tara a Nijeriya ya na gudanar da aikin sa yadda ya kamata.

Anashi banagaran jakada Mbengono ya ce Nijeriya ta taka gagarumin rawa a rayuwar sa, sakamakon yadda ya koyi abubuwa da dama a Nijeriyar.

Da yake taya shugaba Buhari murnar sa ke lashe zabe, ya ce Nijeriya na a hannun mutum nagari, kuma yana farin cikia kan haka.

Leave a Reply