Gwamnatin Nijeriya, ta ce tana sa ido a kan lamarin da ke faruwa a kasar Sudan, bayan sojoji sun hambarar da Gwamnatin Omar Al-Bashir.
Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, ya ce abin da Nijeriya ta damu da shi shi ne, kada a yi rikici kuma a dawo da mulkin dimokradiya nan ba da dadewa ba.
Ya ce har yanzu su na samun labarai a kan abin da ke faruwa, duk da cewa ba su da cikakkun bayanai da alkaluma.
Onyeama ya cigaba da cewa, wannan wani lamari ne da babu cikakken bayani a kan yadda manyan sojojin da su ka jagoranci juyin mulki a Sudan za su mika mulki ga farar hula.
Jami’an tsaro a kasar dai tuni su ka bayyana cewa, hambarar da Al-Bashir tare da sa dokar hana fita za su sama masu lokaci kuma a kawo karshen zanga-zangar.
You must log in to post a comment.