Home Labaru Daukaka Dangantaka: Buhari Zai Karbi Bakuncin Shugaban Kwamitin Wakilan UN

Daukaka Dangantaka: Buhari Zai Karbi Bakuncin Shugaban Kwamitin Wakilan UN

411
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin shugaban kwamitin wakilai na Majalisar Dinkin Duniya, Ms Maria Espinosa wadda za ta kawo ziyarar aiki na kwana guda a Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kwamitin Ms Monica Gravley ne ta sanar da hakan a wujen wani taron manema labarai da aka gudanar a shelkwatan majalisar dake birnin New York na Amurka.
A cewar ta, ziyarar ta kwana guda na daga cikin ziyarar aiki na kwanaki takwas da za ta kawo kasashen nahiyar Afirka ta tsakiya da Afirka ta Yamma.
Kakakin ba ta bayyana abinda shugaban kwamitin wakilai na Majalisar Dinkin Duniya, za ta tattauna da shugaba Buhari ba a ya yin ganarwar ta su, sai dai ta ce za ta ba manema labarai bayyanai kai tsaye a lokacin da ake gudanar da taron.
Gravley, ta ce wasu a fadar shugaba Muhammadu Buhari za su hallarci ganawar kuma daga baya za su gana da daliban jami’an Abuja.
Ana sa ran Espinosa za ta yi jawabi akan hadin kai tsakanin kasashen duniya da kuma yadda za a magance kallubalen da kasashen ke fuskanta sakamakon sauye-sauye da ake samu

Leave a Reply