Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta yi alkawarin hukunta duk wani jami’inta da ta samu da laifin yi wa ‘yan matan da suka kamo daga wajen cashewa Fyade.
Hukumar ta ce yanzu haka ta na jiran wasu mutane ne da ta gayyata wadanda za su bayar da shaida akan ainahin abinda ya faru.
Rundunar ta yi alkawarin hukunta duk wani ‘Dan sanda da ta samu da laifi akan zargin da ‘yan matan da aka kamo a gidan casu suke na cewa wasu daga cikin ‘yan sandan sun yi musu Fyade.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun jami’in ta ASP Danjuma Tanimu, ta ce ta sa kwamiti domin yin bincike akan jami’an ‘yan sandan da ake zargin.
Ya ce sun aika da katin gayyata ga wasu mutane da ake tunanin za su taimaka wurin sanin gaskiyar lamarin, bidiyon kamen da jami’an ‘yan sandan suka yi, ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda ya ke nuni irin cin zarafi da bugu da jami’an ‘yan sandan suka rika yi wa ‘yan matan a lokacin da suka je kama su.
You must log in to post a comment.