Home Labarai Cefane: Tottenham Ta Kammala Ɗaukar Gray Daga Leeds United

Cefane: Tottenham Ta Kammala Ɗaukar Gray Daga Leeds United

46
0
0 GettyImages 1604063299
0 GettyImages 1604063299

Tottenham ta kammala ɗaukar Archie Gray daga Leeds United kan £30m ta kuma bayar da Joe Rodon kan yarjejeniyar £10m.

Gray ya saka hannu kan kwantiragin ne da zai kare a 2030.

Tottenham ta yi wa Brentford shigar sauri, wajen ɗaukar matashin mai shekara 18, wanda ya buga wa Leeds wasa 52 a dukkan karawa a kakar da ta wuce.

Tun farko Brentford ta fara auna koshin lafiyar sa, sai aka ji Tottenham ta biya ƙudin ƙunshin yarjejeniyar sa a ranar Lahadi.

Gray, wanda ya buga wa tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21, zai kuma iya yi wa Scotland wasa.

Rodon ɗan wasan tawagar Wales, wanda ke buga wasannin aro a Leeds United ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka hudu a ƙungiyar.

Leave a Reply