Faransa ta kai zagayen daf da na kusa da na karrshe,
bayan da ta yi nasara a kan Belgium da cin 1-0 ranar Litinin a fafatawar zagaye na biyu a gasar ta Euro 2024.
Faransa ta ci kwallon ta ne saura minti biyar a tashi daga karawar bayan da Jan Vertonghen ya ci gida.
Wannan shi ne karo na 76 da suka fuskanci juna a tsakanin su, inda Belgium ta yi nasara 30, Faransa ke da 27 da canajaras 19,
Da wannan sakamakon, Faransa za ta fuskanci Portugal a karawar dab da na kusa da na karshe wato Kwatafainal a ranar Juma’a 5 ga watan Yuli.