Home Labaru Kasuwanci CBN ya hana a ba wa NNPC Canjin Dala

CBN ya hana a ba wa NNPC Canjin Dala

665
0

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya hana kamfanonin mai sayar wa kamfainin man fetur na kasa (NNPC) dala.

CBN ta hana kamfanonin mai da ke aiki a Najeriya wa NNPC dala  ne, a kokarinta na inganta samar da kudaden kasashen waje a kasar, sakamakon tasirin da annobar da coronavirus ke yi a kan tattalin arzikin kasar.

Asibitin Aminu Kano Ya Dakatar Da Zuwa Dubiyar Marasa Lafiya http://site4.libertyradiogroup.com.ng/asibitin-aminu-kano-ya-dakatar-da-zuwa-dubiyar-marasa-lafiya-2/

Da yake cewa asusun ajiyar kasashen wajen gwamnati ya ragu, Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ce, sabon tsarin fitar da dalan zai bunkasa tare da saukaka samun kudaden waje a cikin kasar.

“Mun shirya inganta hanyoyin samar da dala ga CBN. Mun ba dukkan kamfanonin mai na cikin gida da masu yin harkoki a Najeriya umurni cewa daga yanzu CBN za su rika sayar wa dala ba NNPC ba, domin shigo da albarktun mai daga ketare. Mun kuma fitar da sabon tsarin kayyada farashin dala,” inji shi.

Emefiele ya jaddada muhimmanci inganta tsarin samar da dala ga CBN, mai alhakin samar da kudade waje ga kamfanoni masu shigo da kaya daga waje.

Ya kuma bayyana aniyar bankin na daidaita farshin Naira ta hanyar fito da sabbin tsare-tsare da za su rage yin sayayya da dala t hanyoyi daban-daban.

Leave a Reply