Home Labaru An Rufe Babban Masallacin Abuja Saboda Coronavirus

An Rufe Babban Masallacin Abuja Saboda Coronavirus

657
1
Najeriya na kara daukar matakan dakile yaduwar cutar coronavirus
An rufe masallacin ne domin kawar da taruwar jama'a, daya daga hanyoyin da masana suka ce ana yada cutar

An dakatar da yin sallar Juma’a da sallolin jam’i a Babban Masallacin Kasar Najeriya da ke Abuja domin guje wa yaduwar annobar coronavirus.

Hukumar gudanawar masallacin ta sanar da dakatar da sallolin yau da kullum da na Juma’a a ciki da hararbar masallacin, daga ranar Litinin 23 ga watan Maris da muke ciki, har sai abin da hali ya yi.

Ta kara da cewa za a kuma rufe shaguna da filayen da ke makwabtaka da masallacin.

Sanarwar da ta fitar a ranar Litinin din, ta kuma yi kira ga jama’a su bayar da hadin kai. Cutar coronavirus ta fara kisa a Najeriya yayin d hukumomin lafiya na duniya ke cewa kasar da sauran kasashen Afirka na fuskantar babbar barazana daga annobar.

Matakin rufe masallacin kasar na kama da wanda hukumomin Saudiyya suka dauka da rufe dukkan masallatan Haramin Makka da Madina da sauran masallatan kasar a yunkurinsu na hana yaduwar cutar, wadda ta yi ajalin sama da mutum 1,000 a fadin duniya.

Da farko gwamnatin Saudiyya ta hana shigowar baki da masu aikin Umrah daga kasashe, kafin daukar wasu karin matakai.

A baya-bayan nan ma gwamnatin Saudiyya dokar hana fita a fadin kasar da a nufin hana yaduwar coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutum fiye da 300,000 da suka kamu cutar coronavirus a fadin duniya.