Home Labaru Kasuwanci Bunkasa Noma: Bankin Afrika AFDB Zai Bai Wa Nijeriya Dala Milyan 134

Bunkasa Noma: Bankin Afrika AFDB Zai Bai Wa Nijeriya Dala Milyan 134

111
0

Bankin raya kasashen nahiyar Afrika (AFDB) ya sha alwashin
tallafa wa bangaren noma a Nijeriya da jarin dala milyan 134 da
nufin bunkasa noman kayan abinci.


Shugaban bankin, Akinwunmi Adesina ne, ya bayyana aniyar yayin ziyarar Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri ta Jami’ar
Bayero da ke Kano.


Adesina, ya kuma jaddada muhimmancin samar wa manoma bayanai akan noman zamani, musamman ma yanzu da ake fama
da kalubalen sauyin yanayi.


Adesina, ya bayyana aniyar bankin ta bunkasa ci gaban fasaha a harkar noma.


Ya ce, za su hada kai da cibiyar nazarin noman tsandauri domin inganta ayyukanta a bangaren hasashen yanayi da tattara bayanai, ta haka za su tallafa wa manoma su gudanar da tsare- tsare yadda ya dace.


Ya jinjinawa kokarin shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa sagir Adamu Abbas da daraktan cibiyar nazarin noman tsandauri, Jibrin Muhammad Jibrin saboda tallafin da suke ba manoma wajen yin amfani da fasaha a harkar noma a irin wannan lokaci da ake yaki da sauyin yanayi

Leave a Reply