Home Labarai Tsaro 2: Prof Kailani Ya Tallafawa Jami’An Tsaro Na JTF A Rigasa

Tsaro 2: Prof Kailani Ya Tallafawa Jami’An Tsaro Na JTF A Rigasa

155
0

Shuggaban gamayya kungiyoyin jamiyyun siyasar APC
injiniya Kailani Muhd ya ya bukaci Jami’an tsaro na civilian
JTF àkalla 200 da aka Kaddamar a yankin Rigasa dake Kaduna
su Yi aiki tsakani da Allah.


A lokacin Kaddamar da su , ya gargadisu su, su kasance masu kishin kasa da kishin jama’arsu tare da tabbatar da bin Doka da
oda kamar yadda tsarin aiki ya tanadar.

Prof Kailani, ya ce wannan lokacin na matsalar rashin tsaro ya zama wajibi Alumma su rika ba jami’an tsaro hadin kai domin
samun ci gaba wajen gudanar da ayyukansu.


Sannan ya ce a shekarun baya yankin Rigasa ya Sha fama d matsalar rashin tsaro, Amma da taimakon JTF da sauran jami’asa tsaro lamarin ya zama rarihi Shima Kwamandan na JTF a yankin Rigasa, Malam Aminu ya ja kunnen sauran mambobin kungiyar su yi aiki bisa kwarewa tare ba sauran jamian tsaro hadin wajen aiki.


A wajen kaddamar da Jamain na JTF, Prof Kailani, ya Basu tallafin kudi domin kara karfafa masu gwaiwa wajen gudanar da aiki yadda ya kamata.

Leave a Reply