Home Labaru Barazana: Shugaba Trump Ya Ce Amurka Za Ta Murkushe Iran Idan Ta...

Barazana: Shugaba Trump Ya Ce Amurka Za Ta Murkushe Iran Idan Ta Takulo Ta

406
0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake gargadin kasar Iran ta bi a hankali ko kuma ta murkushe ta a daina jin duriyar ta a doron duniya.

Trump ya yi wannan ja kunnen a shafinsa na Tuwita a ranar Asabar 18 ga Watan Mayu, inda ya kara da cewa, idan har Iran ta na takalar Amurka to karshen ta ya kusa zuwa a duniya.

Donald Trump ya kuma ja kunnan Iran ta guji yi wa Amurka barazana, in kuma ta na da shirin yakar Amurka, to ita ma Amurka a shirya ta ke.

Sai dai, da ake yi hira da shugaba Trump a gidan talabijin na Fox News ya yi la’asar a kan gargadin da ya yiwa Iran , inda ya ce ba za su taba kyale Iran ta rika neman takalar fada a Duniya ba.

Babban jimi’an sojin kasar Iran, Manjo Janar Hossein Salami, ya ce Iran ba ta da niyyar yaki da kowa, amma idan aka kawo mata farmaki za ta tashi tsaye domin kare martabar ta.

Leave a Reply