Home Labaru Diflomasiyya: Shugaba Macron Ya Gayyaci Buhari Zuwa Wani Taro A Faransa

Diflomasiyya: Shugaba Macron Ya Gayyaci Buhari Zuwa Wani Taro A Faransa

364
0

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa wani taron kasashen Afrika da za a yi a watan Yuni.

Sakatariyar taron kasashen Afrika da za a yi a kasar Farance, Stephanie Rivoal, ce ta sanar da hakan yayin da ta ziyarci ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ranar Talata a Abuja.

Ta ce babban makasudin shirya taron mai taken gina birane shi ne, taimakon kasashen Afrika wajen magance matsalar da ta addabi kasashen Afrika ta yawan hijirar da mutane ke yi daga kauyuka zuwa birane.

A cewar ta, ana sa ran Nijeriya za ta gabatar da auyukan da ta yi na gina birane ga masu ruwa da tsaki da za su halarci taron, sannan shugaba Macron na da burin ganin shugaba Buhari ya halarci taron, saboda muhimmancin da Nijeriya ta ke da shi a nahiyar Afrika.

Ta kara da cewa taron zai sha banban da ragowar tarukan da aka saba gudanar wa, saboda za a samar da hanyoyin warware kalubalen da biranen nahiyar Afrika ke fuskanta.

Leave a Reply