Kwamandan rundunar da ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi, ya ce rundunar sa za ta mayar da hankali kan dakile hanyoyin kudin Boko Haram.

Ya ce za su mayar da hankali wurin dakile kasuwancin sayar da kifi da ‘yan ta’addan ke yi a ko ina a kasar nan.
Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Maiduguri kan motocci dauke da kifi da fatan dabobi da aka kwace a Borno bisa zargin masu kayan na kasuwanci da ‘yan Boko Haram.
Ya ce sojojin ba su fice a jihar Borno ba sai dai sun canja salon yakinsu don kare afkuwar hari a sansanin su.
Ya ce sojojin sun rage shingen da suka kafa a cikin gari sun bullo da tawagar soji na gaggawa da ke yawo a gari don magance duk wata matsala da ta taso da ma kare afkuwar hakan.
You must log in to post a comment.