Home Labaru Tsaron Rayuka: Rundunar Sojin Najeriya Ta Ba Kungiyoyin Ba Da Tallafi Tabbaci

Tsaron Rayuka: Rundunar Sojin Najeriya Ta Ba Kungiyoyin Ba Da Tallafi Tabbaci

308
0

Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kudurin da take da shi na tsaron kungiyoyi da hukumomin bada tallafi domin ganin sun ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali da luma a yankin arewa maso gabas.

Kwamandan rundunar ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da ake yiwa lakabi da Operation Lafiya Dole Majo Janar Olusegun Adeniyi ya tabbatar da haka a karshen ganawarsu da wakilan majalisar dinkin duniya dake aikin bada tallafi a Maiduguri.

Adeniyi ya ce rundunar sojin ta dauki sabbin dabaru da za ta rika amfani dasu wajen tabbatar da tsaron lafiya da kayayyakin kungiyoyin dake aiki a yankin.

Ya ce ganawarsu da wakilan majalisar dinkin duniyar da kuma sauran wasu hukumomi da kungiyoyi ya haifar da da mai ido, domin rundunar na aiki ba dare ba rana dan ganin ta yaki ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabas.

Kwamandan ya ce rundunar ta kafa kwamitoci da za su yi aiki ba dare ba rana wajen magance barazanar da ake samu a wasu daga cikin yankunan da ake kai agaji.