Home Labaru Babban Alkali: Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Tabbatar Da Tanko Muhammed

Babban Alkali: Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Tabbatar Da Tanko Muhammed

510
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin tabbataccen Shugaban alkalan Nijeriya

A cikin wasikar da Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar, ya ce bukatar ta biyo bayan shawarar da majalisar alkalan Nijeriya ta bada cewa a tabbatar da matsayin Ibrahim Tanko.

Majalisar Alkalan dai ta bukaci Shugaba Muhamamdu Buhari ya tabbatar da mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin tabbatacen shugaban Alkalan Nijeriya.

An dai cimma matsayar ne yayin wani taron gaugawa da majalisar ta gudanar a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara na Kasa mai shari’a Umaru Abdullahi.

A cikin wata sanarwa da daraktan Yada Labarai na majalisar alkalan Soji Oye ya fitar, ya ce an cimma matsayar ne sakamakon rahoton da kwamitin da aka nada don tantance sabon shugaban alkalan ya gabatar da rahoton sa.