Home Labaru Zaben 2023: Tinubu Ya Nesanta Kan Sa Daga Masu Yi Masa Yakin...

Zaben 2023: Tinubu Ya Nesanta Kan Sa Daga Masu Yi Masa Yakin Neman Zabe

261
0

Jigon jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya nesanta kan sa daga wasu kayayyakin yakin neman zaben shekara ta 2023 da aka yada a titunan birnin Legas da sauran su.

Tinubu ya ce kayan, wanda kungiyar da ke taya shi yakin neman zabe ta ke rabawa gsame da muradin sa na neman kujerar shugaban kasa a shekara ta 2023 bai cancanta ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Tinubu Tunde Rahman, ya bayyana kayan a matsayin wadanda ake rarrabawa ba tare da izinin mai gidan sa ba.

A karshe Tunde Rahman ya ce, Tinubu ba ya da masaniya a kan kungiyar ko kayayyakin da ta ke rarrabawa.