Home Labaru Atiku Ya Yi Martani Kan Korar Karar Da PDP Ta Shigar A...

Atiku Ya Yi Martani Kan Korar Karar Da PDP Ta Shigar A Kan Shettima

99
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku
Abubakar, ya maida martani a kan watsi da karar da jam’iyyar
ta shigar a kan rashin dacewar takarar mataimakin shugaban
kasa na jam’iyyar APC Kashim Shettima.

Kotun kolin dai ta ce ba wani koma-baya ba ne samun adalci a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku Abubakar, ya ce lauyoyin shi sun shirya domin tabbatar da cewa zaben ranar 25 ga watan Fabrairu cike ya ke da magudi.

Ya ce yakin tabbatar da dimokuradiyya da kuma dora sabon tsari na bunkasa ci-gaba a Nijeriya ne wanda ya sadaukar da dukkan abin da ya yi a kai, kuma bai shirya tafiya a kai ba a wannan lokacin da al’umma ke cikin tsaka mai wuya.

Atiku Abubakar, ya yi kira ga magoya bayan shi su yi hakuri, su kuma gudanar da harkokin su cikin lumana yayin da su ke gudanar da shari’ar su a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.

Leave a Reply